A wannan taron koli na farko na shugabannin kasashen Cote d'Ivoire da Ghana , shugabannin biyu sun yi alkawura da dama, musamman na karfafa alakar tattalin arziki da tsaro a tsakanin kasashensu.
A fannin noma da farko, Cote d'Ivoire da Ghana sun yi niyyar hada kai wajen yaki da fasa kwauri a fannin koko, amma da nufin zurfafa hadin gwiwarsu ta fuskar al'adu, tallace-tallace da sarrafa wake.
Shugaban Ghana Nana Akufo Addo da Alassane Ouattara a taron Abidjan © Sia Kambou / AFPHaka kuma a matakin tsaro, Accra da Abidjan na son ci gaba, misali ta hanyar shirya atisayen hadin gwiwa na jami'an tsaro tsakanin kasa da kasa, da kuma kara musayar bayanai.
“Wannan taron ya mayar da hankali ne kan karfafa hadin gwiwar sojojin kasashen biyu.
Koko da ake nomawa a Cote D'Ivoire da Ghana AP - Sophie GarciaShugaba Nana Akufo na Ghana ya bayyana cewa sun himmatu wajen musayar bayanai da musayar fasahohi.”
A matakin yanki, shugabannin kasashen biyu kuma suna son sake kaddamar da muhimmin aikin dangane da batun kudin bai daya na yammacin Afirka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI