Alƙaluman waɗanda ibtila'i ya raba da muhallansu a Afrika ya kusa miliyan 14

Alƙaluman waɗanda ibtila'i ya raba da muhallansu a Afrika ya kusa miliyan 14

Hukumar kula da ƴan cirani ta Majalisar ɗinkin duniyar UNHCR ta ce alƙaluman mutanen da ke rabuwa da muhallansu a yankunan biyu na yammaci da tsakiyar Afrika ya ninka daga mutum miliyan 6 da dubu 500 a shekarar 2019 zuwa mutum miliyan 13 da dubu 700 a shekarar da muke ciki ta 2024.

Hukumar ta UNHCR ta ce akwai fargabar adadin ya iya kai wa miliyan 14 kafin watan Disamban shekarar nan yayinda zai iya zarta miliyan 15 zuwa nan da shekarar 2025.

Daraktan yanki na hukumar Abdourauf Gnon-Konde yayin wani taron manema labarai a birnin Abidjan na Ivory Coast ya bayyana cewa idan alƙaluman zai haɗa da na sauran yankunan bayan na yammaci da tsakiyar ta Afrika, ko shakka babu alƙaluman ka iya zarta tunani lura da cewa yanzu haka akwai mutum miliyan 7 da suka rabu da matsugunansu a jamhuriyyar Congo kaɗai.

Alƙaluman UNHCR ya ce a ƙasar Chadi duk mutum 1 cikin 17 na rayuwa ne ko dai a sansanin ƴan gudun hijira ko kuma matsugunan wucin gadi yayinda ƙasar ke kuma karɓar baƙoncin aƙalla mutane dubu 650 da yaƙi ya koro daga Sudan.

UNHCR ta ce tun gabanin yaƙin Sudan, ƙasar mai yawan jama’a miliyan 17 na da ƴan gudun hijira dubu 420 a wani yanayi da maƙwabtanta da suka ƙunshi jamhuriyar Afrika ta tsakiya da Najeriya da Kamaru dukkaninsu ke fama da matsalolin tsaro.

Haka zalika UNHCR ya kuma gwada misali da yadda matsalolin tsaron yankin Sahel ya raba aƙalla mutane miliyan 4 da rabi zuwa 5 da muhallansu a ƙasashen Mali da Nijar da kuma Burkina Faso.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)