Sojoji 6 sun rasa rayukansu sakamakon harin da kungiyar ta'adda ta Al-Shabab ta kai kan jerin gwanon motocin gwamnan jihar Lower Shabelle, Abdulkadir Sidi.
Bayanan da aka samu aga majiyoyin jami'an tsaro sun bayyana cewa, an kaiwa Sidi hari da safiyar Lahadin da ta gabata a kan hanyarsa ta zuwa fllin tashi da saukar jiragen sama na yankin.
A harin da Sidi ya kubuta ba tare da ko jikkata ba, sojoji 6 sun mutu, wasu sojojin da suka hada da kwamandan dakarun musamman na Somaliya sun jikkata.
An dauki sojojin da suka jikkata zuwa Mogadishu.
Kungiyar Al-Shabab mai alaka da Alka'eda ta bayyana cewar ita ce ta kai harin.
Al-Shabab na yawan kaiwa jami'an tsaro da fararen hula hari yankin.