Shugaban Majalisar koli ta kasar Libiya, Khalid al-Mishri, da Ministan Harkokin Wajen Faransa Jean-Yves Le Drian sun tattauna a Nijer akan batun sojojin kasashen waje a Libiya.
A cewar wata rubutacciyar sanarwa daga Ofishin Sadarwar Majalisar Koli kasar Libiya, Mishri, wanda ya je Nijar don bikin rantsar da sabon zababben Shugaban Jamhuriyar Nijar, Mohamed Bazoum, ya gana da Ministan Harkokin Wajen Faransa Le Drian a babban birnin kasar Yamai.
A taron, an tattaauna akan yiwuwar gudanar da zabe a Libiya a ranar 14 ga Disamba, Majalisar Wakilai ta yi tsare-tsaren doka da suka dace game da zaben, fitar da sojojin kasashen waje daga Libiya da kuma ma akan wasu mihimman abubuwan da suka shafi kasar a halin yanzu.
Misri ya jaddada cewa, ya kamata a ba da fifiko ga ficewar sojojin haya wadanda suke ba bisa ka'ida ba a Libiya, Ya kara da jaddada mahimmancin barin sojojin da aka kawo a kasar da kuma mutuntu yarjejeniyar kasa da kasa ta halattacciyar gwamnatin kasar.
Misri ya kuma ce sojojin da aka kawo kasar ba bisa ka'ida ba barazana ce ga tsaron kasar ta Libya.
An sanar da cewa Ministan Harkokin Wajen Faransa Le Drian ya jaddada cewa ya kamata a janye dukkan sojojin kasashen waje daga Libiya cikin lokaci guda.