Shugaban Majalisar Koli ta Libiya Khalid Al-Mishri ya soki ganawar da Shugaban Rikon Kwarya na Kasar Muhammad Al-Manfi ya yi da dan tawaye Haftar Khalifa a birnin Benghazi.
A sanarwar Khalid Al-Mishri ya fitar ta shafinsa na sada zumunta ya mayar da martani kan ganawar da Manfi ya yi da dan tawaye Haftar.
A sanarwar tasa, Al-Mishri ya ce,
"Muna adawa tare da watsi da ziyarar da Shugaba Al-Manfi ya kaiwa mutumin da ake tuhuma da aikata laifukan yaki Haftar kafin fara aiki a gwamnatance. Wannan ziyara zuwa ga Haftar, ba ta da wani tasiri game da neman hadin kan al'umar Libiya bayan an gama kacalcala su saboda aiyukan da Haftar din ya yi."