Al-Mishri: Dole jama'ar Libiya su jefa kuri'a don amincewa da sabon kundin tsarin mulki
Shugaban Majalisar Koli ta Gudanarwa a Libiya Halik l-Mishri ya bayyana cewa, ya zama wajibi jama'ar kasar su jefa kuri'a don amincewa da kundin tsarin mulki.
Sanarwar da aka fitar daga sashen sadarwa na ofishin gwamnati ta ce, Al-Mishri ya gana da jakadan Italiya a Libiya Giuseppe Buccino Grimaldi a ofishinsa da ke Tarabulus.
A yayin ganawar Al-Mishri ya shaida cewa, dole ne jama'a su jefa kuri'a on amincewa da sabon kundin tsarin mulki, wannan abu zai tabbatar da hana sake samun wani dan kama karya ya shugabanci kasar.
Da yake tabo alakar Libiya da Italiya, Al-Mishri ya nuna bukatar da ke akwai na fadada alakarsu a dukkan bangarori.
Al_Mishri ya kuma yi ni da cewar, ya kamata kamfanunnukan Italiya da suka dakatar da aiyukan gina filin tashi da saukar jiragen sama na Tarabulus da babbar hanyar da ta hada gabashi da yammacin Libiya su dawo bakin aiki.