Al'umar Zambiya na zabar Shugaban Kasa da 'Yan Majalisar Dokoki

Al'umar Zambiya na zabar Shugaban Kasa da 'Yan Majalisar Dokoki

Al'umar Zambiya sun fita rumfunan zabe don zabar Shugaban Kasa, 'Yan Majalisar Dokoki da Shugabannin Yankuna.

Masu jefa kuri'a kimanin miliyan 8 sun fita rumfunan zaben tun karfe 6 na safe tare da fara jefa kuri'a a akwatunan zabe dubu 12.

Shugaban Kasar Zambiya Edgar Lungu na jam'iyyar PF ne ke fafatawa da na jam'iyyar adawa ta UPND Hakainde Hichilema.

Baya ga Shugaban Kasa, jama'ar na Zambiya za kuma su zabi 'Yan Majalisar Dokoki 156 da Shugabannin Yankuna 117.


News Source:   ()