A gobe Litinin 7 ga Disamban 2020, jama'ar kasar Gana za su fita rumfunan zabe don zaben Shugaban Kasa da 'Yan Majalisun dokoki.
'Yan takara 12 ne za su fafata wadanda suka hada da Shugaban Kasar Mai Ci Nana Akupo-Addo da ke neman wa'adi na 2.
Manyan 'yan takarar da za su fafata su ne, Shugaba Nana Akupo-Addo na jam'iyyar NPP da kuma John Dramani Mahama na babbar jam'iyyar adawa ta NDC.
Nana Akupo-Addo mai shekaru 72 na neman wa'adi na biyu kuma na karshe da ya ke da damar yi.
Duk mutumin da aka zaba a matsayin Shugaban Kasar Gana, zai fuskanci matsalolin tattalin arziki, ilimi, makamashi, gina kasa da cin hanci da rashawa.