Yayin wani taron manema labarai a birnin Geneva, shugaban hukumar Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce yanayin yadda cutar ke ƙara yaɗuwa cikin hanzari musamman a jamahuriyar dimokraɗiyyar Congo da maƙwaftanta abin tsoro ne.
A makon da ya gabata Ofisin da ke daƙile yaɗuwar cututtuka a nahiyar Afrika ya sanar da ɓarkewar cutar ta ƙyandar biri a cikin ƙasashe 10, inda ta faro daga Congo, kuma kaso 95 na wadanda cutar ta kama sun rasa ransu.
Ofishin ya kuma ce idan aka kwatanta da lokacin da cutar ta ɓarke a baya, za’a ga adadin kisan da take yi ya ƙaru da kaso 19 cikin 100, sai kuma yawan waɗandan take kamawa da ya ƙaru da kaso 160 cikin 100.
A ranar Alhamis ɗin da ta gabata Ofishin a nahiyar Afrika ya ce akwai yiwuwar nan ba da jimawa ba a ayyana cutar a matsayin annoba a nahiyar Afrika, matuƙar aka ci gaba da samun ƙaruwar masu kamuwa da ita.
Wannan shine kaɗai matakin da zai baiwa ofishin damar amfani da kuɗaɗen da aka tara a baya wajen yaƙi da cutar tare da samar da rigakafi da kuma magunguna don takaita yaɗuwa da kuma yadda take hallaka jama’a ba ji ba gani.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI