Akwai buƙatar kawo karshen rikicin Sudan - Amina Mohammed

Akwai buƙatar kawo karshen rikicin Sudan - Amina Mohammed

A yayin ziyarar da ta kai kan iyakar Chadi don ganewa idonta yadda ayarin motocin kayan agajin suka shiga cikin kasar a ranar Juma’a, Amina Mohammed ta ce akwai bukatar kawo karshen yakin da aka kwashe tsawon lokaci a nayi a Sudan.

Idan dai ba a mataba a lokacin tattaunawar warware rikicin da aka yi a birnin Geneva, bangarorin da ke gwabza rikicin sun fara cimma matsaya, duk da dai basu amince da bada damar shigar da kayan agaji ta manyan iyakokin kasar biyu ba.

A wata sanarwar bayan taron da Hukumar samar da abinci ta Duniya ta fitar a ranar Alhamis, ta ce manyan motoci dauke da kayan abincinta da ya kai tan dari 630, wanda zai iya wadata mutane dubu 55, sun samu damar shiga kasar daga Chadi.

Tun a tsakiyar watan Afrelun shekarar data gabata ne dai yaki ya barke a Sudan, tsakanin sojojin kasar da ke karkashin jagorancin Janar Abdel Fattah al-Burhan da kuma na RSF da ke karkashin tsohon mataimakinsa Mohamed Hamdan Daglo.

Kungiyoyin bada agaji sun ce rikicin ya hana bada damar kai wa mutane miliyan 25 da ke cikin matsananciyar yunwa kayan abinci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)