Akalla mutane 50 ne aka kashe a tsakiyar kasar Sudan

Akalla mutane 50 ne aka kashe a tsakiyar kasar Sudan

Rahotanni na nuni cewa tun a watan Afrilun shekarar 2023 Sudan ta fada cikin yaki tsakanin dakarun RSF karkashin jagorancin Janar Mohamed Hamdane Daglo da kuma sojojin karkashin jagorancin Janar Abdel Fattah al-Burhane, shugaban kasar.

Yakin dai ya yi sanadin mutuwar dubun dubatar mutane, inda aka yi kiyasin daga 20,000 zuwa 150,000,ba tare da samu adadin mutanen da suka jikkata ba.

"An kai hari kauyukan al-Sariha da Azraq da ke yankin jihar Al-Jazeera," in ji kwamitin Hasaheisa Resistance Committee, wata kungiya mai fafutukar tabbatar da dimokuradiyya da ke shirya taimakon juna tsakanin mazauna yankin.

A cikin al-Sariha, an kashe mutane 50,wasu da dama suka jikkata a jiya Jumma'a, a cewar kungiyar, wanda ta ba da rahoton rashin yiwuwar " kwashe wadanda suka jikkata,saboda tashin bama-bamai.

Wasu daga cikin yankunan da dakarun RSF suka kai hari Wasu daga cikin yankunan da dakarun RSF suka kai hari REUTERS - Staff

Ba za a iya bayar da adadin mutanen da ke makwabtaka da kauyen Azraq ba, amma kwamitin ya ce an yi masa kawanya gaba daya, mutanen yankin yanzu haka na fuskantar cin zarafi.

A baya-bayan nan dai dakarun sa-kai sun tsananta cin zarafi kan fararen hula a jihar Aljazeera da ke kudancin birnin Khartoum inda ake da manoma da dama.

Wani sansanin dakarun kasar Sudan Wani sansanin dakarun kasar Sudan AP - Sam Mednick

Kungiyar ta koka matuka ganin halin da ake ciki biyo bayan,katsewar hanyoyin sadarwa, a halin yanzu ba zai yiwu a tabbatar da ainihin adadin mutanen da suka rasa rayukan su a wannan al'amari.

Kungiyar likitocin Sudan a jiya Juma'a ta yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta matsa lamba don samar da hanyoyin samar da agaji ga kauyukan da ke fuskantar kisan kiyashi a hannun mayakan kungiyar RSF yayin da ayyukan ceto suka gagara.

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)