A wani mataki na karfafa matakan tsaro rundunar yan sanda sun kara yawan ma’aikatan su a wadanan yankuna da lamarin ya shafa.
A jiya Juma’a ne ministan harkokin cikin gida Kithure Kindiki ya ayyana yankuna 12 a yankin Tana River a matsayin masu hadari da tashin hankali, ciki har da garin Bura inda fada ya fi kamari.
Wasu daga cikin unguwanin da ambaliya ta ritsa da su a kasar Kenya © APShugaban ‘yan sandan Kenya, Douglas Kanja, ya bukaci mazauna yankin da su mika makamansu domin kaucewa barkewar rikici. Matsalolin sun fara ne a lokacin da gwamnatin karamar hukumar ta ba da filaye domin daukar mutanen da suka rasa matsugunansu sakamakon ambaliyar ruwa a kogin Tana, kogin mafi tsawo a Kenya. Mazauna yankin sun yi zanga-zangar, inda suka jaddada cewa makiyayan za su mamaye wuraren kiwo nasu.
Wasu daga cikin iyayen da suka rasa ya'an su REUTERS - Monicah MwangiWani babban jami’in ‘yan sanda a gundumar Tana River y ana mai bayyana cewa “Mun yi asarar mutane 18 tun a watan da ya gabata, an kuma kara samar da tsaro domin hana mutuwa.”
Jami’in da ya bukaci a sakaye sunan sa ya na mai bayyana cewa" a halin yanzu ana fargabar barkewar wani sabon rikici saboda mutane sun ki mika makamansu."
A yau Asabar, darektan binciken laifuka Mohamed Amin ya sanar da kama wasu shugabannin kananan hukumomi biyu, gwamnan lardin Dhadho Godhana da dan majalisa Said Hiribae, saboda rashin amsa sammacin 'yan sanda game da tashin hankalin.
An lalata gidaje da dama sannan wasu mutane da ba a san adadinsu ba sun tsere daga yankin.
Wani mazaunin Bura, Mohamed Ibrahim ya koka da cewa: "Ba sa jin dadi a nan, wasu hare-hare ma suna faruwa da rana. “Duk saboda filaye ne.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI