Shugaba Tinubu ya faɗi haka ne yayin ganawa da takwaransa na Rwanda Paul Kagame a birnin Abu Dhabi na haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.
Tinubu ya ce dole ne su mayar da hankali kan ƙarfafa alaƙar cikin gida domin bunƙasa kasuwanci da haɗin kan ƙasashen Afrika, saboda al’ummarta da nahiyar su amfana.
Haka zalika, shugaban Najeriyar ya ce akwai tarin albarkatun ƙasa a yankin Afrika, mutane da kuma ƙarfin da za ta iya tsayawa da ƙafarta, ba tare da dogaro da ƙasashen duniya ba.
Tinubu da Kagame na ziyara a Abu Dhabi ne domin halartar taro na tsawon mako guda na samar da ci gaba mai ɗorewa, daga 12 zuwa 18 ga watan Janairun shekarar 2025.
A halin yanzu dai ƙasashen Afrika na fama da talauci da rashin hadin ƙai tare da bukatar masu zuba jari daga kowanne yanki na duniya, wanda ake ganin abu ne mai wuya su iya kawo ci gaban yankin a ƙashin kansu ba tare da hadin kai da wasu kasashen duniya ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI