Afrika ta samu alluran rigakafin ƙyandar biri miliyan guda - WHO

Afrika ta samu alluran rigakafin ƙyandar biri miliyan guda - WHO

A cewar WHO alluran kusan miliyan guda sun isa ga ƙasashe 9 waɗanda aka samu ɓullar cutar inda a ƙasashen Jamhuriyar Congo mahaifar cutar da kuma maƙwabciyarta Rwanda kaɗai aka yiwa mutane fiye da dubu 50 rigakafin cutar.

Babban daraktan WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus a jawabinsa game da rarraba alluran rigakafin ya godewa ƙasashen da suka tallafawa nahiyar da alluran rigakafin ciki har da Amurka da Tarayyar Turai.

Kalaman na Ghebreyesus na zuwa a dai dai lokacin da cibiyar yaƙi da cutuka masu yaɗuwa ta Afrika CDC ke cewa an samu ƙaruwar yaɗuwar cutar da akalla kashi 500 a bana idan an kwatanta da yanayin yaɗuwar cutar a bara.

CDC ta ce a yanzu haka akwai cutar a ƙasashen nahiyar ta Afrika 19 waɗanda kuma kowannensu ke ganin yawaitar alƙaluman sabbin harbuwa.

Cikin watan Agustan shekarar nan ne WHO ta ayyyana dokar ta ɓaci kan cutar ra ƙyandar biri bayan ɓullar wata sabuwar nau’i da ta fantsama ƙasashen maƙwabta daga Congo.

A cewar Ghebreyesus a wannan makon ma akwai allurai dubu 900 amma za a rabbasu bisa ga yanayin buƙatar kowacce ƙasa musamman waɗanda suka samu ɓullar sabon nau’in na claude b.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)