Afrika ta kudu za ta ƙarbi ragamar shugabancin ƙungiyar G20

Afrika ta kudu za ta ƙarbi ragamar shugabancin ƙungiyar G20

Wannan ne karon farko da wata ƙasa a Afirka za ta karbi shugabancin ƙungiyar mai ƙasashe 20 mafiya ƙarfin tattalin arziƙi a duniya.

Afirka ta kudu za ta jagoranci ƙungiyar har zuwa ƙarshen shekarar 2025, lokacin da Amurka za ta karbi jagorancin daga hannunta.

Ƙasashen na G20 sun ƙudiri aniyar magance matsaloli da sauyin yanayi ka iya haifarwa, yayin da tashe-tashen hankula ke ƙara ta’azzara a faɗin duniya.

Idan za’a iya tunawa dai a watan Nuambar wannan shekara ta 2024 ne  ƙasashen suka haɗu domin tattaunawa kan matsalolin da duniya ke fuskanta, tare da fidda matsayarsu.

Cikin bukatun da G20 suka fitar har da na gaggauta kawo ƙarshen yunwa, yaƙe-yaƙe, musamman na Gaza, da kuma na Ukraine.

Yayin da suka kuma ƙaddamar da haɗakar ƙasa da ƙasa don yaƙar talauci da yunwa.

Kana, sun tattauna dangane da sauyin da za a gani na manufofin Amurka akan hulɗa tsakaninta da ƙasashe, sakamakon sabuwar gwamnatin shugaba mai jiran gado Donald Trump dake shirin fara aiki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)