Afrika na jimamin rasuwar Issa Hayatou tsohon Shugaban hukumar CAF

Afrika na jimamin rasuwar Issa Hayatou tsohon Shugaban hukumar CAF

Rasuwar Issa Hayatou a Paris ta zo dai dai lokacin da kungiyoyin kwallon kafar Afrika dake wakiltar Nahiyar a gasar Olympics na Paris ke kafa tarihi,wanda ya zo wani lokaci da kungiyar kwallon  kafar Morocco ke samun lambar tagulla bayan da ta doke Masar a faggen tamola.

An dai fuskanci jita -jita dangane da rasuwar wanan jigo a faggen tamola a nahiyar ta Afrika,sai dai sanarwa a hukumance ta tabbatar da rasuwar Issa Hayatou dan kasar Kamaru.

Tsohon Shugaban hukumar kwallon kafa ta Caf,Issa Hayatou. Tsohon Shugaban hukumar kwallon kafa ta Caf,Issa Hayatou. AFP PHOTO / FADEL SENNA

Jim kadan bayan sanar da wannan rashi, sakonni suka soma isowa daga sassan daban daban na Duniyar nan ,kama daga Shugaban hukumar kwallon kafa ta Duniya Gianni Infantino,da wasu kusushin a faggen tamola da suka san mammacin ,a nahiyar Afrika,shugaban kwallon kafa Patrick Motsepe dan kasar Afrika ta kudu cikin jimami ya bayyana cewa Afrika ta yi rashin daya daga cikin mutanen da suka asasa kwallon kafa tsawon shekaru.

Inda muka duba tarihin mammacin an haife shi ne a ranar 9 ga Agusta, 1946 a garin Garoua, a arewacin Kamaru, ya sadaukar da yawancin rayuwarsa ga ƙwallon ƙafa na Afirka.

Issa Ayatou,Tsohon Shugaban hukmar kwallon kafa ta CAF Issa Ayatou,Tsohon Shugaban hukmar kwallon kafa ta CAF Photo: Pierre René-Worms / RFI

Marigayi Issa Hayatou ya share kusan shekaru 30 a shugabancin hukumar ta CAF ,kafin a shekara ta 2017 ya fuskanci wata gugguwa da ta kai shi ga zabe a lokaci inda ya sha kayi daga hannun dan kasar Madagascar Ahmad Ahmad.

Wani abu lura shine marigayi tun ya na matashi yake shawar tsere da wasannin motsa jiki,duk da cewa  ya fito daga gidan sarauta, domin mahaifinsa Sarkin musulmi ne,kuma ana sa ran zai gaji mahaifin na sa,sai dai babban da sauren dangin na sa ya rugumi bangaren kwallon kafa.

Tsohon Shugaban hukumar kwallon kafar Afrika, Issa Hayatou. Tsohon Shugaban hukumar kwallon kafar Afrika, Issa Hayatou. AFP PHOTO/FADEL SENNA

Ya fara taka leda a wasannin guje-guje da tsalle-tsalle kuma ya zama zakaran Kamaru a kan mita 400 da 800, har ma ya halarci gasar farko ta Afirka a tarihi a Brazzaville a 1965. A lokaci guda kuma, ya kasance memba na kungiyar kwallon kwando ta Kamaru da kuma kwallon kafa na jami'o'in kasa da kasa.

Tarihi ya nuna cewa a karkashin shugabancinsa ne kasar ta Kamaru ta lashe kofin Afrika na kwallon kafa a 1988.

Hakan na daga cikin mayan abubuwan da suka taimakawa, Issa Hayatou ya zama shugaban CAF na biyar a watan Agustan 1987, inda ya maye gurbin marigayi Ydnekatchew Tessema na Habasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)