Afirka ta kudu za ta fara bai wa ƴan Najeriya bizar shekaru 5

Afirka ta kudu za ta fara bai wa ƴan Najeriya bizar shekaru 5

Ramaphosa ya bayyana wannan mataki a matsayin wani ɓangare na ƙara ƙarfafa alaƙa tsakanin Najeriya da Afrika ta Kudu, lokacin buɗe taron hukumar haɗin gwiwa tsakanin Najeriya da Afirka ta Kudu karo na 11 a jiya Talata, a birnin Cape Town na ƙasar .

Shugaba Ramaphosa ya ce hakan zai sauƙaƙa tafiye-tafiyen ƴan kasuwa da masu yawon buɗe ido zuwa ƙasar, ta hanyar samun bizar shekaru 5 fiye da sau 1.

Cyril ya yi alƙawarin cewa Afirka ta kudu za ta cire ka’idoji kan sanya hannun jari, tare da magance matsalolin da kamfanoni ke fuskanta na ƙasashen biyu.

A bayanin bayan taro da suka fitar ya nuna cewa, ƙasashen biyu sun ƙarƙare tattaunawar kan yarjejeniyar shekaru 5 ta musayar bayanai akan matsaloli na aikata manyan laifuka, barazanar tayar da hatsaniya, da kuma cin zarafi ƴa ƴan ƙasashen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)