AFCON 2025: Yadda 'yan wasan Najeriya suka shafe sama da sa'o'i 10 a filin jirgi

AFCON 2025: Yadda 'yan wasan Najeriya suka shafe sama da sa'o'i 10 a filin jirgi

Tawagar manyan 'yan wasan kwallon kafar Najeriya ta isa filin tashi da saukar jiragen sama a ranar Lahadi, inda maimakon su sauka a filin jirgin sama na Benghazi, sai aka ajiye su a filin jirgi na Al Abraq.

Kyaftin din tawagar, William Troost-Ekong, wanda ya bayyana halin da ake ciki a shafinsa na X a ranar Litinin, ya bayyana rashin jin dadin yadda suka yi zaman sama da sa’o’I 12, amma hukumomin da abin ya shafa a Libya sun yi biris da su.

Ya kuma kara da cewa wani direban bas da ya isa filin jirgin, tare da wasu ma’aikata, ya yi ta jifansu da kalamai na ba’a da shagube yana musu dariya.

Ekong ya ce abin da ya girgiza su shine, bayan ma’aikatan sun ce musu babu man jirgi, sai kuma matukin jirgin ya shaida musu cewa akwai mai a tsawon lokacin da suka dauka suna zaune.

Gwamnatin Najeriya, ta hannun Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar, da Ministan wasanni, John Enoh, da shugabar hukumar da ke lura da ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje, Abike Dabiri-Erewa, sun yi Allah wadai da wannan mummunan lamari.

Bugu da kari, 'yan wasan Super Eagles da suka hada da Victor Osimhen, Victor Boniface da mai tsaron gida Stanley Nwabali, duk sun nuna rashin jin dadinsu kan lamarin.

Sai dai har yanzu hukumar kwallon kafa ta Afirka bata ce komai akan wannan al’amari da ya ja hankalin magoya bayan kwallon kafa a sassa daban-daban na duniya ba.

Tawagar Super Eagles dai ta yi tattaki zuwa Libya ne domin buga wasa a zagaye na biyu na wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka da za a yi a 2025, bayan ta karbi bakuncin tawagar Libya a makon jiya.

Bayan kai ruwa ranar da aka yi a filin jirgin saman na Al Abraq ne, hukumar kwallon kafar Najeriya ta yanke shawarar cewa Super Eagles, ba za su buga wasan da aka tsara fafatawa a ranar Talata ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)