A yau Lahadi ne hukumar bayar da agaji ta Mozambique ta sanar da ƙaruwar adadin mutane 94 da suka rasa rayukansu daga 76 da aka sanar a baya, sakamakon iftili’an ƙaƙƙarfar guguwar Chido da ta afkawa wasu ƙasashen yankin tekun Indiya.
Guguwar wadda ta haifar da asarar rayuka a tsibirin Mayotte na Faransa, baya ga wasu dubbai ko kuma ɗaruruwa da suka yi ɓatan dabo, ta kuma lalata gidaje sama da dubu 110 a Mozambique.
Iftila'in na zuwa ne bayan da ƙasar ta kudancin Afrika ta yi fama da munanan rikice-rikicen bayan zaɓe, wanda jam’iyya mai mulkin ƙasar tun bayan da ta samu ƴancin kai daga Portugal, ta zargi jam’iyyar adawa da kitsa maguɗi a zaɓen.
Wannan dai ba shi ne karon farko da Mozambique ke fuskantar ibtila'in guguwa cikin shekarar nan ba, domin ko a baya-bayan nan guguwar ta hallaka tarin mutane wanda ya tilasta kwashe al'ummomin da ke zaune a gab da tsaunuka ko kuma bakin ruwa.
A baya bayan ne Asusun Bada Lamuni na Duniya IMF ya sanar da cewa rikicin siyasa da guguwar Chido ya mayar da tattalin arziƙin Mozambique baya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI