A rahotonta da ƙungiyar ta IPC da majalisar Ɗinkin Duniya ta yi bitarsa ta fitar, ya nuna cewa mutane dubu dari 6 da 38 ne ke fuskantar matsananciyar yunwa yanzu haka a Sudan, yayin da wasu miliyan 8 da dubu ɗari ke gab da fuskantar matsalar.
Rahoton ya nuna cewa matsalar ta yunwa ta bazu zuwa wasu sansanonin ƴan gudun hijira a yankunan yammaci da kuma kudancin ƙasar.
Tun a ranar litinin ne dai gwamnatin Sudan ta sanar da fitarta daga cikin duk wani shiri na duba matsalolin yunwa a duniya, wanda ake ganin hakan zai haifar da koma baya wajen samun alkaluman wadanda matsalar ta shafa.
Wata 20 ke nan aka kwashe ana gwabza rikici a Sudan tsakanin sojojin ƙasar da kuma na RSF, lamarin da ya ƙara ta’azzara ayyukan jin kai.
Rikicin da aka faro a watan Afrelun bara, ya lakume rayukan daruruwan mutane, tare da sanya sama da miliyan 12 gudun hijira, adadin da Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana a matsayin mafi yawa da rikici ya haifar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI