Adadin mutanen da suka mutu a gobarar da ta tashi a wata makarantar Kenya ya karu

Adadin mutanen da suka mutu a gobarar da ta tashi a wata makarantar Kenya ya karu

Gobarar da ta tashi a makarantar Hillside Edarasha da ke gundumar Nyeri ta tashi ne da tsakar daren ranar Alhamis a wani dakin kwanan dalibai da yara sama da 150 ke kwana. Makarantar, wacce ke hidimar dalibai kimanin 800 masu shekaru 9 zuwa 12 ko 13, tana cikin wani yanki da ke kusa da kauye mai nisan kilomita 170 daga arewacin Nairobi babban birnin kasar.

Wasu daga cikin iyayen da suka rasa ya'an su Wasu daga cikin iyayen da suka rasa ya'an su REUTERS - Monicah Mwangi

Shugaban kasar Kenya William Ruto ne ya bada umarnin zaman makoki na kwanaki uku daga ranar litinin 9 ga watan Satumba, bayan mutuwar yara akalla mutane 21 a daren ranar Alhamis 5 zuwa Juma'a 6 a sakamakon gobara da ta tashi a makarantarsu ta kwana, dake tsakiyar kasar.

Mkarantar Hillside Endarasha da ke yankin Nyeri na kasar Kenya Mkarantar Hillside Endarasha da ke yankin Nyeri na kasar Kenya © Raphael Ambasu / AFP

Wasu bayyanai daga masu bincike na nuni cewa da alama katsewar wutar lantarki ne ya janyo wannan gobara a dakin kwanan daliban na wannan makaranta.

Wannan dai ba shine karo na farko da kasar ta Kenya ta fuskanci irin wannan matsala ba, ta sha fama da irin wannan bala'I don ko a shekarar 2017, harin kone-kone da aka kai a makarantar sakandaren ‘yan mata ta Moi da ke birnin Nairobi ya yi sanadiyyar mutuwar dalibai 10. A shekarar 2001, a gundumar Machakos da ke kudu maso yammacin kasar, yara 67 ne suka mutu sakamakon gobara da ta tashi a dakin kwanan su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)