Adadin mutanen da suka mutu sakamakon fashewar wasu abubuwa a garin Bata na Equitorial Guinea sun karu zuwa 98.
Mataimakin Shugaban Kasar Teodoro Nguema Obiang Mangue ya shaida cewa, sakamakon ibtila'in da ya afku a ranar 7 ga Maris, adadin wadanda suka mutu ya kai mutane 98 yayinda 615 kuma suka samu raunuka.
Sakamakon fashewar wasu abubuwa a barikin soji na Nkoa Ntoma da ke garin Bata, gidaje da dama sun rushe tare da danne jama'a.
An bayyana cewa, akwai yiwuwar fashewar ta afku a ma'ajiyar makaman da ke barikin sojin.