Adadin ƴan ci-rani da suka tsallaka zuwa turai daga Afrika ya haura dubu 63 a 2024

Adadin ƴan ci-rani da suka tsallaka zuwa turai daga Afrika ya haura dubu 63 a 2024

Shekara ta biyu kenan a jere ana ganin ƙaruwar kwararar ƴan ci-ranin da ke tsallakawa tsibirin na Canary a Sifaniya a wani yanayi da jumullar ƙasashen Turai suka karɓi yawan baƙin haure marasa rijista da yawansu ya kai dubu 63 da 970 daga adadin dubu 56 da 852 da suka kwarara zuwa nahiyar a shekarar 2023.

Sifaniya na matsayin ƙasar da ta fi ganin shigowar ƴan ci-rani a kaf cikin takwarorinta ƙasashen Turai, lamarin da ya sanya ta tsaurara matakai a mashigIn tekun Mediterranean. 

Sai dai baƙin hauren kan yi amfani da ɓarauniyar hanya wajen kwarara cikin ƙasar galibi daga gaɓar ruwan ƙasashen yammacin Afrika zuwa tsibirin na Canary a tafiya mai cike da haɗari.

Hukumar kula da iyaka ta EU ta ce an samu raguwar baƙin haure marasa rijista da ke kwarara ƙasashen nahiyar da aƙalla kashi 40 tsakanin watan Janairun bara zuwa Nuwamba, sai dai an ga ƙaruwar waɗanda ke kwarara ta ruwa musamman tekun Atalanta galibi ƴan ƙasashen Mali da Senegal da kuma Morocco.

A bara ne aka ga hauhawar ƴan ci-ranin da ke shiga tsibirin na Canary mafiya yawa tun bayan tururuwar da aka gani a shekarar 2006.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)