Ɗumamar yanayi a duniya ce ta ta’azzara ruwan sama a yankunan Nijar da Tafkin Chadi da ƙarin kashi 5 zuwa 20 fiye da yadda ya ke kafin yanzu, a cewar ƙungiyar World Weather Attribution, wata tawagar masana kimiyya da ke nazari a kan nasabar sauyin yanayi da yanayi mai tsanani da ake fuskanta a duniya.
Ɗaya daga cikin masanan, Izidine Pinto ya ce a halin da ake ciki yanzu, irin ruwan sama mai ƙarfi da ake kwararawa a sassan Sudan, Najeriya, Nijar, Kamaru da Chadi ya zama wai sabon abin da zi ci gaba da zame wa al’ummomin yankin jiki.
Masana kimiyyar sun ce idan dumamar yanayi ya kai digiri 2 a ma’aunin celcius, ko kuma 3 da ɗigo 6 a ma’aunin Fahrenheit, wanda zai iya aukuwa nan da shekarar 2050, za a iya ci gaba da samun mamakon ruwan sama a duk shekara, su na mai kira a zuba kudi a cikin tsarin gargaɗi tun kafin lokaci ya ƙure, da kuma gyarar madatsun ruwa.
A wannan shekarar, ambaliyar ruwa ta yi sanadin mutuwar kimanin mutane dubu 1 da ɗari 5 a ƙasashen yammaci da Tsakiyar nahiyar Afrika, a cewar hukumar agaji ta Majalisar Ɗinkin Duniya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI