Abdelmadjid Tebboune ya lashe zaben Algeria da kashi 94.65% na kuri'u

Abdelmadjid Tebboune ya lashe zaben Algeria da kashi 94.65% na kuri'u

Daga cikin jimillar kuri'u miliyan 5.6 da aka rubuta, miliyan 5.320 ne suka zabi Abdelmadjid kamar dai yadda  Mohamed Charfi, shugaban hukumar zaben kasar ya sanar.

Shugaban hukumar zaben Algeria a yau lahadi ne gaban manema labarai ya kawo Karin haske dangane da jinkiri da aka fuskanta gkama daga jiya yan wajen tattara sakamakon wannan zabe da wasu yan kasar ke cewa an tafka ba dai dai ba.

Takardar zaben Algeria Takardar zaben Algeria © AFP

Wani dan karamin bincike ya bayyana kauracewar matasan kasar,sai dai wasu yan kasar ta Algeria na fatan ganin  Abdelmadjid Tebboune ya ci gaba da mulki da kuma aiwatar da sauye-sauye.

Shugaban Algeria Abdelmadjid Tebboune yan lokuta bayan fitar da sakamakon zaben Shugaban Algeria Abdelmadjid Tebboune yan lokuta bayan fitar da sakamakon zaben © AFP

"Duk wanda aka zaba za a yi maraba da shi, Abdelmadjid Tebboune ko wani dan takara a cewar wani bangaren na al’uma.

 Babban abin da ke faruwa shi ne cewa kasar na samun ci gaba kuma kasar Algeria ta zama kasa mai ci gaba daidai da sauran kasashe inji wani shugaban kungiyar kare demokkuradiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)