Caccakar dai na zuwa ne bayan hukumomin ƙasar sun tilastawa mutanen da suka maƙale fitowa daga mahaƙun na tsawon watannin dan su fuskanci hukunci.
Ya zuwa yanzu an zaƙulo gawarwakin mutane 60 baya ga wasu 132 a raye, ko da ya ke akwai wasu ɗaruruwan mutane da suka maƙale a ƙarƙashin ƙasar.
Sai dai kuma jam’iyyar haɗaka ta Democratic Alliance ta yi kira da a gudanar da binciken ƙwaƙwaf wanda zai haɗa irin matakin da jami’an tsaron ƴan sanda suka ɗauka na wuce makaɗi da rawa, wanda ya haɗa da hana kai wa mutanen kayayyakin agaji kamar su abinci da ruwa tun cikin watan Agustan zuwa Disamban bara bayan hukuncin kotu.
Mahukuntan na Afrika ta kudu na ci gaba da kamewa tare da tsare dukkanin mahaƙan da aka ceto daga cikin ramukan waɗanda ta ce galibinsu ƴan cirani ne da suka shigo ƙasar ba bisa ƙa’ida ba, kuma sun karya dokoki da dama.
A cewar gwamnatin, mahaƙan na yi mata zagon ƙasa ta fuskar tattalin arziƙi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI