A Sanagal za a binne gawar tsohon Shugaban Kasar Chadi Hissene Habre da ya mutu a ranar Talatar nan.
Matar Habre Fatima Habre Raymonde ce ta fitar da sanarwa game da batun.
Sanarwar ta ce, iyalan Habre ba su bukaci wani abu daga wajen gwamnatin Chadi ba.
Bayan mutuwar Habre, kakakin gwamnatin Chadi Abdurrahman Koulamallah ya ce, idan ana so za a iya kai gawar Habre zuwa Chadi.
An tsare Hambararren Shugaban Kasar Chadi Habre a gida na kwanaki 60 bayan barkewar Corona a watan Afrilun 2020, daga baya kuma aka dawo da shi kurkuku.
A shekarar 2017 aka yankewa Habre hukuncin daurin rai da rai a shari'ar da aka yi masa a Kotun Musamman ta Tarayyar Afirka. Kotun ta same shi da laifukan yaki da keta hakkokin dan adam a lokacin da yake mulki.
A shekarar 1982 Habre ya yi juyin mulki tare da hawa mulkin Chadi, a 1990 kuma Shugaban Kasar Chadi Idris Deby Itno da aka kashe a fagen daga a ranar 19 ga Afrilun 2021 ya hambarar da gwamnatin Habre.
A shekarar 2013 aka kama Habre tare da gurfanar da shi a gana kotu a kasar Sanagal da yake neman mafaka, a watan Yulin 2015 ya gurfana a gaban kotu tare da fuskantar hukuncin daurin rai da rai.