An sanar da nada sakatariyar shugaban kasar Togo watau Victoire Dogbe Tomegah a matsayar firaiministan kasar.
Shugaban kasar Togo Faure Gnassingbe ya sanar da nada Victoire Dogbe Tomegah a matsayar firaiministan kasar bayan murabus din stohon firaiministan Komi Selom Klassou.
Tomegah dai ta kafa tarihi akan kasancewarta firaiminista mace ta farko da aka taba yi a kasar. An bayyana cewa a cikin 'yan kwanakin dake tafe za ta bayyana sabbin majalisar ministocin kasar.