Ministan lafiyar kasar Samuel-Roger Kamba ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Kinshasa babban birnin kasar cewa, "Za mu kaddamar da shirin rigakafin daga gobe asabar 5 ga watan Oktoba, a maimakon ranar Laraba da ta gabata,cutar wanda a baya ake kiranta da cutar kyandar biri,an jinkirta soma allurar ne musamman saboda jinkirin da aka fuskanta wajen isar da alluran wannan kasa.
Yankin Goma na DRCongo ReutersA cewar Mistan lafiya ta wannan kasa, za a yi allurar rigakafin farko a Goma, babban birnin lardin Kivu ta Arewa, ga nau'o'in al'ummar da ake ganin sun fi fuskantar hadari kamar ma'aikatan lafiya, da masu mu'amala da marasa lafiya.
Gabashin DRCongo shi ne yankin da cutar ta fi shafa. Gabaɗaya, ƙasar ta sami fiye da mutane 30,000 da suka kamu da cutar, aka kuma samu mutuwar kusan 990 tun farkon wannan shekara tare da karuwar mace-mace tsakanin yara, 'yan kasa da shekaru biyar," in ji ministan lafiyar kasar.
Wasu daga cikin mutanen da suka kamu da cutar Mpox © Reuters / Ngendakumana EvrardKasar ta DRCongo ta sami allurai 265,000 a watan da ya gabata daga Tarayyar Turai da Amurka. Wadanan alluran rigakafin, wanda dakin gwaje-gwaje na Danish Bavarian Nordic ya ƙera, an yi su sabili da maya a cewa likitocin.
Wani maganin rigakafi na mpox, wanda za a iya ba wa yara, Japan ce ta ba da izini, wanda DRCongo ke cikin tattaunawa don yuwuwar wadata.
Ministan ya bayyana cewa buƙatun sun fi girma, a wannan ƙasa mai mutane miliyan 100, baiwa kasar allurai 265,000 ba za su iya magance matsalar ba", in ji Ministan Lafiya na DRCongo.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI