A Cote D’Ivoire an soma sake fasalin gyaran sunayen masu zabe

A Cote D’Ivoire an soma sake fasalin gyaran sunayen masu zabe

 

 A halin yanzu alkaluma da ake da su a hukumar zaben kasar na nuna cewa mutanen da abin ya shafa sun kai kusan miliyan 8.12.

Alkauma da wasu yan siyasa a kasar suka bayyana matukar damuwa a kai,wanda a baya ya haifar da tarzoma a tsakanin su na ganin an sake fasalin zaben ga baki daya.

Birnin Abidjan na kasar Cote D'Ivoire Birnin Abidjan na kasar Cote D'Ivoire © AFP/Issouf Sanogo

A Cote d'Ivoire, aikin na sake fasalin jerin sunayen zaɓe na da nufin shigar da yawan masu jefa ƙuri'a gwargwadon iko. Hukumar zabe mai zaman kanta (CEI) ta bude karin wuraren yin rajista: hukumar ta bayyana cewa daga cibiyoyi 10,000 za ta samar da cibiyoyi 12,000.

Simone Gbagbo, Shugabar jam'iyyar MGC a kasar Côte d'Ivoire Simone Gbagbo, Shugabar jam'iyyar MGC a kasar Côte d'Ivoire AFP - SIA KAMBOU

 A daya bangaren a wani mataki na kawo sauki ga yan kasar da ke bukatar mika sunayen su ga hukmar zabe,hukumomin sun sanar da yiwa jama’a takardar shaidar ɗan ƙasa kyauta,wanda zai baiwa jama’a damar samun yin rijista.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)