Kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch ta bayyana cewa akalla mutane 30 ne aka kashe a kasar Mozambique a yayin aka shafe kusan makonni uku ana zanga-zangar adawa da zaben shugaban kasa mai cike da takaddama.
Wannan adadin da aka fitar bai hada da na wanda aka gabatar a ranar 7 ga watan Nuwamba ba a lokacin da ‘yan sanda da sojoji suka tarwatsa dubban masu zanga-zanga a Maputo babban birnin kasar.
Al'ummar ƙasar dake kudancin Afirka dai na fama da tashe-tashen hankula ne tun bayan da jam'iyyar Frelimo da ta shafe kusan shekaru 50 tana mulki ta lashe zaben da aka gudanar a ranar 9 ga watan Oktoba da sama da kashi 70 na kuri'un da aka kada.
Ana sa ran shugaba Filipe Nyusi zai sauka daga mulki a farkon shekara mai zuwa a karshen wa'adinsa na biyu, inda zai mikawa Daniel Chapo.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI