48 ne suka mutu sakamakon ruftawar wata tsofuwar mahakar zinari a Mali

48 ne suka mutu sakamakon ruftawar wata tsofuwar mahakar zinari a Mali

Kasar Mali dai na daya daga cikin ƙasashen da ke kan gaba wajen samar da zinari a nahiyar Afirka, kuma wuraren da ake haƙar ma'adinai a kai a kai ana fuskantar zabtarewar kasa da kuma hadurra.

Hukumomin kasar sun yi ta kokawa kan yadda ake hako karafa masu daraja a kasar ba tare da ka'ida ba.

A wasu alkaluma daga hukumomin tsaron kasar an samu mutuwar mutane da dama a baya ,wanda ya sa hukumomi daukar matakan  hana hako zinarin ba bisa ka’ida ba,sai kuma wannan hadari na rasa mutane 48 wanda ke dada tabbatar da cewa,duk da matakan sa ido ,wasu yan bata gari na gudanar da aikin ba tareda bin doka ba.

Wasu daga cikin yankunan da ake hako zinare a kasar Mali Wasu daga cikin yankunan da ake hako zinare a kasar Mali © OUSMANE MAKAVELI/ AFP

Ana ci gaba da neman wadanda abin ya shafa, kamar yadda shugaban wata kungiyar kare muhalli ya shaidawa AFP.

Haɗarin na ranar Asabar ya faru ne a wani wurin da aka watsar da wani kamfani na kasar China a da, kamar yadda majiyoyi suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP ke aiki a kasar ta Mali.

A watan Janairu, wata zaftarewar kasa a wata mahakar zinari da ke kudancin kasar Mali ta kashe mutane akalla 10 tare da bacewar wasu da dama, mafi yawansu mata.

Sama da shekara guda da ta wuce, wani rami ya rufta a wani wurin da ake hakar zinare  inda mutane sama da 70 suka mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)