28 ga watan Satumba,ranar 'yancin zubar da ciki ta duniya- matsalar a Congo Brazzaville

28 ga watan Satumba,ranar 'yancin zubar da ciki ta duniya- matsalar a Congo Brazzaville

A kasar ta Congo Brazzaville,rahotanni na nuni cewa a babban birnin Brazzaville, mutane na kashe kudi a zubar da ciki a ɓoye  tsakanin 10,000 zuwa 50,000 CFA francs (ko tsakanin Yuro 15 zuwa 76).

 Ana gudanar da haka a cikin yanayi mara kyau kuma sakamakonsa yana da yawa, kamar dai yada kungiyoyi da dama suka tabbatar tare da yin kira ga kasashen Duniya na ganin sun kawo dauki kasar ta Congo.

Unguwar Poto-Poto a Brazzaville Unguwar Poto-Poto a Brazzaville AFP - MONIRUL BHUIYAN

Da jimawa hukumomin kasar suka dau matakan haramta gudanar da zubar da ciki ta bayan fage,sai dai duk da wadanan matakai,wasu asibitoci na ci gaba da gudanar da irin wadanan ayuka da ke janyo rasa rayuka na iyaye mata,wanda kungiyoyi ke ci gaba da kokawa a kai yanzu kam.

Birnin Ouesso, na kasar Congo-Brazzaville Birnin Ouesso, na kasar Congo-Brazzaville © Wikiemdia Commons/CC BY-SA 4.0/OUesso

Kasar ta Congo Brazzavile ta yi kaurin suna a batun da ya shafi zubar da ciki daga cikin kasashen Africa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)